Wednesday, 18 October 2017

Allah abin godiya: Mun samu Canji

Allah sarki rayuwa shigen irin yanda jami'an tsaro kewa mutane kenan a wasu jihohin Arewacin kasarnan a duk lokacin da aka samu harin bom ko na 'yan bindiga a shekarun baya, kana fita daga gidanka gabanka na faduwa, kana cikin taron jama'a Allah-Allah kake ka fita kar wani mummunan abu ya ritsa dakai, hatta sallah idan kanayi a masallaci idan tayar mota ta fashe ko kuma leda ta fashe sai cikinka ya kada.Cikin ikon Allah da kuma amsa addu'o'inmu da yayi yau gashi an samu sauki sosai kwanciyar hankali da nutsuwa ta fannin tsaro suna kara samuwa zaka fita ka nemi abinci, kaje gurin aiki da duk wata hidima taka ba tare da kana tunanin tashin bamba irin na baya.

Allah mun godema da wannan ni'ima daka mana, muna rokon ka yaye mana sauran matsalolin da muke fama dasu a kasarnan badan halayenmu ba.

No comments:

Post a Comment