Tuesday, 31 October 2017

Allah sarki: Karanta wasiyyar da wannan yarinyar ta bari: Ta nemi gafarar kowa a ciki

Wata yarinya 'yar shekaru 16 me suna A'isha ta rubuta wasiyyar neman gafarar iyayenta, abokanta da malamanta kamin ta rasu, wani dan uwantane ya saka labarin da kwafin wasikar data rubuta a dandalinshi da facebook, yace ta rasu ranar Juma'ar data gabata a garin Kaduna.

A cikin wasikar ta A'isha hadda wani dake binta bashi ta fada, inda tayi rokon a biyashi kuma tayi rokon da iyayenta da abokanta da sauran 'yan uwanta suyi mata addu'a idan ta rasu.

Wannan labari ya dauki hankulan mutane sosai kuma an yi ta yiwa A'ishar addu'ar neman gafara da saduwa da Rahamar Allah
Ya Allah ka gafartawa A'isha da dukkan sauran 'yan uwa Musulmi baki daya.

No comments:

Post a Comment