Thursday, 26 October 2017

Allah sarki Malamin makaranta: Ya hana diyarshi Auren wanda take so sobada malamin makarantane

Wannan gajeren bidiyon da aka yanko daga wani fim din Hausa ya dauki hankulan mutane sosai a dandalin sada zumunta da muhawara bayan da wani bawan Allah ya wallafashi a dandalinshi, bidiyon ya nuna magidancine da iyalanshi a zaune 'diyarshi ta gayamai cewa ta samu wanda take so, sai ya tambayeta wai shi wannan da kike so din aikin me yake yi, sai ta bashi amsa da cewa malamin makarantane, irin yanda suka nuna firgici da wannan zabi na 'diyar tasu ya bayyana cewa sun yi mamaki da yanda 'yar masu arziki irinsu za ta kawo malamin makaranta da sunan wanda zata aura.Mutane da dama sun yi ta nanata wannan bidiyo da kuma danna alamar sonshi, wasu da sukayi sharhi akan wannan bidiyon sun bayyana cewa ya basu dariya, wasu kuwa sun nuna takaici da irin yanda aka wulakanta aikin koyarwa yanda ba kowa bane yake son diyarshi ta auri malami ba.

Wasu kuwa sun bayyana cewa kwarya ta bi kwarya, kar ka kai kanka inda kasan za'a wulakanta ka ko kuma a maka kallon banza, ka nemi daidai da kai.

Domin fahimtar cikakken abinda bidiyon ya kunsa sai a kalleshi.

Allah ya kara rufa mana Asiri Duniya da Lahira.

No comments:

Post a Comment