Friday, 13 October 2017

"Allah ya hadaki da Momo a Arewa24 zaki tauna cingam da kyau>>Wata ta gayawa Maryam Gidado

Mutane sai a barsu, tun bayan da fitaccen jarumin finafinan Hausa kuma me gabatar da shirye-shirye na tashar Arewa24 kuma jarumin jarumai na shekararnan da muke ciki wato 2017, Aminu Sharif, Momo ya yiwa jaruma Umma shehu tambayar bazata akan wadda ta shayar da annabin tsira(S.A.W) amma ta kasa bayar da amsa, da yawa mutanen gari da masu sharhi sun ta bayyana ra'ayoyi akan wannan batu wasu sunyiwa 'yan fim din kudin goro wasu kuwa kushe Aminu sharif sukeyi, to yanzu abin ya kai ga har anawa 'yan fin din tsiya da barazana akan haduwa da Aminu Sharif, Momo idan sukayi wani abin, fitacciyar jarumar fina finan Hausa Maryam Gidado ta saka wani gajeren hoton bidiyo a dandalinta na sada zumunta, abinda wata ta gayamata zai baka dariya.Bayan da Maryam ta saka wanan hoton bidiyon na sama, sai wata tace mata "hahaha Allah ya hadaki da Momo a Arewa24 zaki tauna cingam da kyau".

Hmmm wannan abu sai a hankali.

No comments:

Post a Comment