Monday, 9 October 2017

Aminu Ala Yasa shahararren dan film dinnan Malam Isa Bello Ja kuka.


A jiyane da akayi taron gamayyan masoyan Alh. Aminu Ladan Abubakar (Ala) a filin wasa na makarantar Ado Gwaram jihar Kano, wanda masoyan Mawakin suka shirya. Mawakin yayi Wakar bazata ga farin Dattijon ayayin taron wanda hakan ne yasa Datijjon mamaki da kukan farin ciki. Allah ya kara Dankon zumunci.

WAKA.
MALAMI DA KE KOYAR DA MU
MALAMIN DA KE FADAKAR DA MU,
HAZIKIN DA KE NUSAR DA MU,
JARUMIN DA KE GOGAR DA MU,
SAHIBIN DA KE ZAN CE DA MU,
SHUGABA DA KE ZAMNI DA MU,
DALIBIN DA KE KOYO DA MU,
MASANIN DA BAI RAINA MU, MU.
BABA BELLO YA NARKE DA MU,
BA SHI NUNA KYAMA SHI DA MU.

No comments:

Post a Comment