Friday, 13 October 2017

Aminu Sharif Momo ya karyata Sadik Sani Sadik

Fitaccen jarumin finafinan Hausa, me gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arewa24 Aminu Sharif Momo ne ya lashe kyautar jarumin jarumai na shekarar nan ta 2017 wadda masu karrama fitattun mutane na City People Award suka bashi, to saidai a kwanakin baya fitaccen jarumin finafinan Hausa Sadik Sani Sadik ya gayawa bbchausa cewa idan dai yana masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood babbu wanda zai kara cin gasar jarumin jarumai idan bashiba(idan baka karanta wannan labariba danna nan).


A nan dai Aminu Sharif yace wannan magana ba haka takeba domin kuwa ya lashe kyautar City People Award wadda tana daya daga cikin wadda jarumai ke son ganin sun samu, saidai mu jira wasu kyautukan muga ko Sadik din zai lashe?.

No comments:

Post a Comment