Sunday, 22 October 2017

An Gano kofar Wuta a kasar Saudiyya

Wani zaice Toh fa! Wadannan kuma zasu jawomana abinda yafi karfinmu, toh wannan labari haka kafafen watsa labarai da yawa musamman na ketare suka wallafashi, wani gurine aka gano a kasar Saudiyya wanda babu koda ciyawa ko wata bishiya ko kuma wata dabba a kusa da gurin, wadanda suka gano gurin sunce wasu kofofine da aka yisu da duwatsu da kuma narkakken ruwan dutse, a kintacensu sunce wadannan kofofi sun kai kimanin shekaru dubu tara.Amma duk da haka kamar yanzu aka yisu babu wata alamar cewa ya dade ko kuma ya fara tsufa, su kansu wadanda suka gano gurin ta irin tauraron dan adamdinnanne dake sararin samaniya suka ganoshi, amma sunce nan bada dadewaba zasu san yanda zasuyi domin su matsa kusa da gurin dan kara samun gamsasshen bayani  akan wannan sabon guri da aka gano.

Irin yanda wadanda suka gano gurin sukayi bayaninshi da kuma hotunan da suka wallafa yasa kafafen watsa labarai da kuma wasu masu sharhi suka rika bayya wannan guri da cewa kofar wutane.

Akwaidai gurare da yawa a Duniyarnan da ake musu irin wannan lakabi da cewa kofar Wutane, saboda mutane da masu bincike sun kasa gano menene ainihin gurin ko kuma saboda sarkakkiyar dake tattare da irin wadannan gurare, nan gaba idan Allah ya yarda shafin hutudole.com zai binciko wadannam gurare ya kuma wallafa dan karuwarmu gaba daya.

Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment