Friday, 13 October 2017

An kaddamar da mashina masu tashi sama a Dubai

Inda ake yin abu ana yinshi, a watan daya gabatane mukaji labarin cewa Dubai ya kaddamar da motoci masu tashi sama, sai kuma gashi yanzu Dubaidin ya sake kaddamar da mashinan 'yan sanda masu tashi sama, hukumomi sun bayyana cewa an kaddamar da wadannan mashinanne domin jami'an tsaron su samu saukin bin masu karya doka da kuma kaiwa ga guraren da keda cinkoson ababen hawa cikin sauki wanda idan da motane zaiyi wuya.Allah kasa wataran muga irin wadannan abubuwan cigaba a kasarmu Najeriya.No comments:

Post a Comment