Sunday, 8 October 2017

An karrama jaruman finafinan Hausa da kyautuka a gurin bayar da kyauta na City People Award

An karrama jaruman finafinan Hausa a gurin bayar da kyautuka ga mutanen da suka nuna hazaka da akeyi na City People Award duk shekara, wadanda aka karrama sune kamar haka:

Ali Nuhu(Sarki) ya samu kyautar wanda ya samu gagarumar cigaba a rayuwarshi.

Aminu Sharif(Momo) ya samu kyautar jarumin jarumai na shekara.

Lawal Ahmad ya samu kyautar me taimakawa babban jarumi na shekara.


 Kamal S. Alkali ya samu kyautar fitaccen me bayar da umarni na shekara.

Ibrahim Dady ya samu kyautar jarumin jarumai na finafinan Series wato wadanda akeyi masu dogon labari na shekara da kuma kyautar jarumin da yafi nuna kwazo da ake ma kallon zai samu gagarumar cigaba nan gaba.

Sai kuma Rashida Labbo wadda itace ta samu kyautar jarumar jarumai ta mata na finafinan Series wato masu dogon labari.

Sai kuma Umar M. Sharif wanda ya lashe kyautar jarumin jarumai na sabbin fuskoki.

Sai kuma Ahmad Ali Nuhu wanda ya lashe kyautar jarumin jarumai na yara masu tasowa.

Sai kuma Hajara Isah wadda ta samu kyautar jaruma da tafi nuna kwazo da akema kallon zai samu gagarumar cigaba nan gaba.

Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment