Thursday, 26 October 2017

An nada dan tsohon shugaban kasa IBB, Aminu Babangida shugaban bankin Unity Bank

An nada dan gidan tsohon shugaban kasa Aminu Babangida a matsayin shugaban bankin Unity Bank, a yau Alhamis, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa biyo bayan kammala aiki da tsohon shugaban bankin yayine hukumar gudanarwar bankin ta nada Aminu Babangida a matsayin sabon shugaba wanda dama shine mataimakin shugaban bankin.Aminu dai 'da ne a gurin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, mutane sun yita fadin daga jin dadi zuwa jin dadi, to haka Allah yake abinshi, idan shi Aminu dan tsohon shugaban kasane to shi tsohon shugaban kasar dan wanene?

Allah yasa mu dace.

No comments:

Post a Comment