Saturday, 28 October 2017

An nada Rashida Mai-Sa'a Sarautar Wakiliyar Arewa, Fati Nijar kuma Gimbiyar Arewa

A ranar Alhamis din data gabatane kungiyar masu shirya fina-finai reshen jihar Naija suka yiwa fitacciyar jarumar fina-finan Hausa kuma me baiwa gwamnan jihar Kano shawara a bangaren harkokin mata Hajiya Rashida Adamu Mai-Sa'a nadin Sarautar Wakiliyar Arewa, haka kuma kungiyar ta nada tauraruwar mawakiya Fati Nijar Sarautar Gimbiyar Arewa.


Jaruman finafinan Hausa irin su Hadizan Saima , Saima Muhammad, A'isha Haruna Kalo sun masu rakiya zuwa gurin nadin Sarautar.
Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment