Thursday, 26 October 2017

An samu kuskuren rubutu a takardar neman Afuwa da Rahama Sadau ta rubuta

A jiyane labarin takardar bayar da hakuri da neman afuwa da fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta rubuta zuwa ga hukumar kula da harkokin finafinai da kuma hakurin da ta bayar a wani gidan rediyo na Kano ya karade shafukan sada zumunta ka kafofin labarai na kasarnan musamman Arewa, Wasu sun zauna suka yiwa takardar tankade da rairaya inda suka gano kura-kurai a cikin rubutun takardar.Andai rubuta takardar da Turancine kuma Rahama Sadau ta saka hannu akan takardar, watau ita ta rubuta kenan, wadanda suka gano kura-kuren sun fito da wasu ka'idojin rubutu da Turancine wadanda ba'a bisu ba wajan rubuta takardar da kuma wasu kalaman Turancin da ba'a rubutasu daidai ba a cikin takardar, Rahama Sadau dai ta kammala kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, Kaduna Polytechnic inda ta samu shedar karatu ta babbar Difiloma.

.....Saidai kuma za'a iya cewa kowa zai iya yin kuskure kuma Turanci ba yarenmu bane duk daga baya muke koyonshi.

Ga inda aka samu kura-kuren a takardar ta Rahama Sadau.

No comments:

Post a Comment