Saturday, 28 October 2017

An samu sabon me kudin Duniya

Me shafin yanar gizo na Amazon daya shahara wajan sayar da kaya ta yanar gizo watau Jeff Bezos ya sake zama wanda yafi kowa kudi a Duniya inda ya doke wanda yake akan matsayin na yanzu watau Bill Gates me kamfanin Microsoft, Benzos ya samu wannan cigabane banyan da farashin hannun jarin kamfaninshi ya tashi sama jiya Juma'a hakan kuma yasa dukiyar da Benzos din ke da ita takai dalar Amurka biliyan casa'in da miliyan dari shida, shi kuma Bill Gates yana da dalar Amurka biliyan casa'in da miliyan dari daya.Watanni uku da suka gabata Benzos ya taba zama wanda yafi kowa kudi a Duniya bayan da farashin kamfaninshi yayi tashin gwauron zabin da bai taba yiba amma cikin 'yan awanni ya rikito Bill Gates ya sake darewa matsayin.

Shin ko yanzuma zai dade akai ko kuwa zai sake rikitowa? 'Yar manuniya zata nuna.

No comments:

Post a Comment