Friday, 20 October 2017

An shiryawa Fati Muhammad walimar taya murnar samun karin girma a gidauniyar tallafawa jama'a ta Atiku Care

Wasu masoyan tsohuwar fitacciyar jarumar finafinan Hausa Fati Muhammad sun shirya mata walima yau Juma'a a Otal din Aso dake kan titin Waff na garin Kaduna, sun shirya taron walimarne domin tayata murnar samun karin girma da tayi daga me kula da harkokin mata na gidauniyar tallafawa mutane ta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shiyyar jihar Kaduna zuwa me kula da harkokin mata na yankin Arewa maso yamma gaba daya.Daya daga cikin abokan aikinta ya bayyana cewa jajircewa data nuna a tsohon mukamin da aka bata yasa ta samu wannan karin girma cikin kankanin lokaci.

Jaruman finafinan Hausa na da dana yanzu da yawane suka halarci wannan kasaitacciyar walim, Tahir I. Tahir da Abbas Sadik ne suka jagoranci gudanar da wannan Walima, Adam A. Zango, Rabi'u Rikadawa,  Fati Washa Sa'adiya Gyale, Fati K.K, Hauwa Waraka, Binta kofar Soro dadai sauran manyan jarumai sun halarci gurin wannan walima da sauran 'yan uwa da abokan arziki, muna taya Fati murna da fatan Allah ya kara daukaka.
No comments:

Post a Comment