Sunday, 22 October 2017

An yabawa kasar hadaddiyar daular larabawa bisa nada matasa da tayi a mukaman siyasa

Wani abin sai a makwabta, Kasar hadaddiyar daular larabawa, UAE a takaice tayi wasu nadae-naden mukaman gwamnati wanda cikin wadanda aka nada ministoci hadda matasa 'yan shekaru ashirin da bakwai da kuma talatin, wanda da wuya a samu irin haka a Nahiyarmu ta Afrika ko kuma a Najeriya, wannan matashin da ake ganin hotonshi a sama sunanshi Omar Al Olama kuma an nadashi karamin ministan kirkire-kirkiren zamani na kasar hadaddiyar daular larabawan.Sai kuma wannan itama me suna Sarah Al Amiri 'yar shekaru talatin da haihuwa wadda aka nada mukamin ministar kimiyya da fasaha, bincike da sauransu.

Wannan nade-nade yasa mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta na zamabi suka rika yabawa kasar saboda saka matasa cikin harkokin mulki, a lokaci guda kuma suka rika fatan samun haka a kasashensu.

No comments:

Post a Comment