Saturday, 14 October 2017

Ana wata ga wata: Hirar Umma Shehu tasa an tono inda Bilkisu Abdullahi itama ta kwabsa

Tohfa tone-tone ya taso tun bayan da hirar da Aminu Sharif Momo yayi da Umma Shehu ta watsu inda yayi mata tambaya akan wadda ta shayar da annabi amma bata bayar da amsaba, hakan yasa wasu sukace ai ba Ummarce kadai ta taba kwabsawaba a shirin da Aminu Sharif din yake gabatarwaba, akwai wata jaruma da ake kira da Bilkisu Abdullahi itama Momo din ya taba mata tambayar a ina ta tsaya a karatu amma bata bayar da amsa daidaiba.


Gadai yanda abin ya kasance.


Tsakure a cikin wata tattaunawa da Aminu Shariff Momo ya yi da sabuwar Jarumar Finafinan Hausa mai suna Bilkisu Abdullahi.

Momo: Ina kika tsaya a karatu?


Bilkisu: Na karanta "Business Admin" a Secondary School. Yanzu kuma ina jiran yayana ya sayo min form a Jam'ia.

 KannywoodExclusive

No comments:

Post a Comment