Wednesday, 25 October 2017

Ashe Reno Omokri ya iya Hausa?

Tsohon me baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fannin kafofin watsa labarai watau Reno Omokri kuma sanannen me sukar gwamnatin shugaba Buhari musamman ta kafafen sada zumunta na zamani ya baiwa mutane mamaki jiya a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin twitter inda yayi rubutu da Hausa.Andai saba ganin rubun na Reno da Turanci kwatsam jiya sai gashi yayi rubutu akan batun Maina da Hausa inda ya rubuta cewa.
"EFCC sun zata mu yara ne, sun jira tukun kafofin watsa labarai su yi kuka kafin suka rufe gidan Maina. Ba su san adireshin da suka gabata ba?"

Wani ya tambayeshi cewa "Ranka ya dade ashe kana jin Hausa haka?"

Sai ya mayar mishi da amsa cewa"a koyo nike...na gode."

Hmmm gaskiya yayi kokari.

No comments:

Post a Comment