Saturday, 28 October 2017

Auren diyar Bukola Saraki: Manyan mutane sun halarta:An dauke wuta a gurin bikin

A yaune aka yi baikon diyar shugaban majalisar dattijai Olutosin Halima Saraki da Angonta Olatunde Olukoya a Otal din Eko dake birnin Legas, Auren dai wanda aka shirya yinshi a jihohi uku Kwara da Legas da Abuja, kafar watsa labarai ta Sahara Reporters tace uban Amarya Bukola Saraki ya shirya kashe makudan kudi da suka haura naira biliyan daya dan kece raini a bikin diyar tashi.Wani labari kuma da Saharar dai ta wallafa tace ana cikin shagalin bikin na Diyar Sarakine sai ba zato babu tsammani aka dauke wutar Lantarki wanda hakan ya jefa manyan mutane dake gurin cikin fargaba.

Manyan mutanen da suka halarci gurin wannan Baiko sun hada da mataimakin shugaban kasa da matarshi, Farfesa Yemi Osinbajo, Dolapo Osinbajo da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da sanata Ben Bruce da hamshakin attajirin dan kasuwa Aliko Dangote da kuma wasu sauran fitattun mutane.

A makon daya gabatane wani ya fito ya soki Bukola Sarakin akan aurar da diyarshi da zaiyi ga wanda ba musulmi ba a matsayinshi na musulmi tunda addini ya hana hakan kuma mutumin yace wannan aure zai karya karfin siyasar Bukola Saraki musamman a Arewa.

No comments:

Post a Comment