Sunday, 22 October 2017

Ayyukan sabuwar gidauniyar dake so ta mayar da yara mata masu talla akan tituna makaranta zasu fara kankama

A jiyane mukaji labarin tsohuwar fitacciyar jarumar finafinan Hausa, matar Sani Danja, Zaki watau Mansurah Isah da mawaki Morell sun zama jakadun wata gidauniya me suna Green Heart, wadda zata mayar da hankali akan ganin yara mata masu talla a kan tituna sun ajiye farantan tallar tasu sun koma makaranta, to da alama ayyukan gidauniyar zai fara kankama gadan-gadan.A wadannan hotunan za'a iya ganin Mansurah Isah tare da wasu mata da yara sun dora wasu kaya masu kama da kayan makaranta a kawunansu wanda hakan ke nuni da cewar za'a maye farantin talla da litattafan ilimi.


No comments:

Post a Comment