Sunday, 1 October 2017

Ba zan taba yarda a raba Nigeria ba>> Shugaba Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai taba amincewa da kiraye-kirayen da wadansu 'yan kasar suke yi na ballewa ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a jawabinsa na ranar bikin cika shekara 57 da samun 'yancin kasar.Najeriya ta samu 'yancin kai ne daga hannun Turawan Birtaniya a shekarar 1960.
"A lokacin da nake matashin soja, na ba da gudummuwata tun daga farko har karshen yakin (Basasar Najeriya) wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kimanin miliyan biyu, ya kuma haddasa azaba da barna mai yawa," in ji Shugaba Buhari.

Ya ci gaba da cewa wadanda suke kiraye-kirayen maimaita hakan (a yanzu) ba a haife su ba lokacin yakin don haka ba su da masaniya game munanan abubuwan da yakin ya jawo wa al'umma, kamar yadda ya ce.

Hakazalika ya ce bai jin dadin yadda wadansu jagorori a yankin da son ballewa "ba sa jan kunne matasan da suke ci gaba da son a raba Najeriya" musamman game da abin da hakan ka iya jawo wa.

Daga nan shugaban ya ce sulhu shi ne mafita kan duk wani al'amari. Sai ya bukaci "duk wanda yake da wani korafi game da kasar da ya gabatar da shi ga majalisar dokoki ta kasar da kuma majalisun dokoki na jihohi."

Ya ce amma ba wadansu kungiyoyi "marasa kan gado ba."


Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-Delta don samun dawwamanman zaman lafiya a yankin.

"Muna da niyyar magance sahihan matsalolin al'ummomin yankin," in ji shi.

Kan batun tsaro

Shugaban ya yaba da wa dakarun kasar kan galabar da suke samu a kan mayakan Boko Haram.

"Dole mu gode wa zakakuran sojojinmu kan yadda suka fatattaki 'yan Boko Haram, suka samu nasara a kansu kuma rage yawan hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."

Daga nan ya ci gaba da cewa "ba za mu yi kasa a gwiwa ba." Ya ce an fara fadada aikin rundunar Lafiya Dole da take aiki a yankin arewa-maso- gabashin kasar.

Har ila yau ya gode wa makwabtan kasashe da sauran kasashen duniya game da taimakon da suke ba "kasar a fagen yaki da ta'addanci."

Hakazalika ya ce gwamnatinsa tana "aiki ba dare, ba rana" wajen ganin an 'yanto sauran 'yan matan Chibok da sauran mutanen da ke hannun 'yan Boko Haram.

"Gwamnati za ta taimakawa dakarun kasar nan ba kawai a yaki da ta'addanci ba, amma har da matsalolin satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manona," a cewarsa.

Tattalin Arziki

Shugaban ya bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa take yi wajen ganin kasar ta rage dogaro kasokan kan man fetur.

bbchausa.

No comments:

Post a Comment