Sunday, 15 October 2017

Badakalar Umma Shehu: Nazir Ahmad, Sarkin Waka ya fitar da bidiyo dan karar da mutane ilimi akan wadda ta shayar da Annabi(S.A.W)

Bayan daya saka wani hoton bidiyo wanda yayi bayanin cewa ya kamata mutane su rika bincikar abu kamin suyi sharhi kokuma magana akanshi, wanda yayi kira da cewa bai kamata mutane su yankewa Umma Shehu hukunci da gajeruwar hirar da akayita watsawaba, wanda haka yasa mutane da dama suka zargeshi da goyon bayan Ummar wasu kuma sunce maganarshi gaskiyace, Fitaccen mawakin Hausa Nazir Ahmad (Sarkin waka) ya saka fitar da wani bidiyon inda yace wannan bawai na goyon bayan Umma Shehu bane, ya yishi ne domin ya karar da mutane ilimi akan wadda ta shayar da Annabi(S.A.W) bayan rasuwar mahaifiyarshi.Nazir yace ilimifa kamar manjane da yawan malamai idan aka tambayesu sai sunje sun dan tasheshi haka kuma yace yasan da yawa idan aka tambaya zasuce Halimatu Sa'adiya, bawai ba haka bane.....

Domin jin cikakken abinda yace sai a saurari gajeren bidiyon sama.

No comments:

Post a Comment