Saturday, 14 October 2017

Badakalar Umma Shehu: Ummi Zee ta yiwa Umma Shehu kaca-kaca/tsiya

A lokacin da abokan aikin Umma Shehu ke kokarin kareta akan abin da ya faru da ita na hirar da Aminu Shafrif Momo yayi da ita a Arewa24 inda ya tambayeta wadda ta shayar da Annabi(S.A.W) amma bata bayar da amsaba har mutane ke kiranta da Jahila, Ummi Zeezeee itama ta shiga sahun mutanen gari domin kuwa ta yiwa Umma Shehun kaca-kaca a wani bayani da tayi a dandalinta na sada zumunta.A cikin bayanin da Ummi Zeezee tayi ta saka hoton hannunta rike da kudi ta rubuta cewa " Suna da dadin kashewa saidai ba albatka, daga mutum ya bude bandir daya shikenan a awa daya zata kare inya fita yawo...Allah ka sawa kudin kasarmu albarka kamar na sauran kasashen Duniya"

Bayan tayi wannan rubutune sai wasu masoyanta/masu sharhi suka juya abin zuwa maganar Umma Shehu duk da basu kira sunaba amma sun rika fadin cewa dama wata ta biyawa kudin Islamiya ta samu lada, ita kuma Zeezee sai ta biye musu suka ta kada baki tace ai koda ta biya ba amfani tunda kan ya cushe da dusa, haka dai sukaita yiwa Ummar tsiya.

Ga karin yanda abin ya kasance:

No comments:

Post a Comment