Tuesday, 17 October 2017

"Baka iya turanci ba">>Hadiza Gabon ta sake dankarawa wani Magana

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ta sake gayawa wani daga cikin mabiyanta magana mara dadi a dandalinta na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter, Mutumin yayi rubutu da harshen turanci inda yacewa Hadizar"Ke Hadiza Gabon mutane na jin tsoron yimiki magana saboda kinajin (cewa) ke watace, kina zaginsu", sai Hadizar ta mayar mishi da martanin cewa"Gashi baka iya turanci ba. Muyi Hausa kawai dan uwa, Nima turancin nawa beyi karfiba/lallabawa nikeyi".


Duk da yake cewa a kwai gyara a turancin mutumin da ya yiwa Hadizar magana, Aikuwa da yin wannan magana ta Hadiza sai ta fara yaduwa mutane nata sake nanata sakon anata sharhi akai, wasu dai sunce ai turancinma yarene kamar yaren Hausa saboda haka ba wani kayan gabas bane

A makon daya gabatane Hadizar ta dankarawa wani magana akan yace mata tayi aure, sai tacemai sai babanshi ya saki mamanshi tazo ta auri baban nashi.

No comments:

Post a Comment