Monday, 23 October 2017

"Ban taba yin karatun boko ba amma masu digiri da digirgir na aiki a karkashina">>Muhammad Indimi

Hamshakin attajirin dan kasuwa kuma sirikin shugaban kasa Muhammad Indimi a cikin wata tattaunawa da yayi da kafar watsa labarai ta premium times yace bai taba shiga aji da sunan yin karatun boko ba a rayuwarshi amma gashi masu digiri da digirgir na aiki a karkashin kamfaninshi.Muhammad Indimi yace babu malamin daya taba koya mishi koda "A" da sunan karatun boko, duk abinda ya koya ya koyane wajan maida hankali a mu'amalar da yakeyi da mutane da kuma masu ilimi.

Ya kara da cewa manyan ma'aikata a kamfaninshi idan zasu kawomai maganar wani aiki da za'ayi sai sun tabbatar sun yishi da kyau idan ba hakaba zasu zo yana musu gyara a cikin aikin nasu.

No comments:

Post a Comment