Saturday, 7 October 2017

"Bazan taba daina yin fim din Hausaba har sai randa na mutu, Masu shiryawane basa sakani a sabbin finafinai">>Maryam Booth

Da alama rashin fitowar fitacciyar jarumar finafinan Hausa Maryam Booth wadda ake kira da Dijan gala a cikin finafinan kwanannan ya fara damunta dama wasu daga cikin masoyanta, domin kuwa a wani yanayi me nuna alamar damuwa da mayar da amsa, Maryam din tayi wani rubutu a dandalinta na sada zumunta da muhawara inda tace masu tambayarta cewa wai ko ta bar masana'antar finafinai na Hausa to su sani cewa tana nan daram.Ta kara da cewa batayi niyyar daina yin fim din Hausa ba kuma bata da niyyar dainawa haka kuma ba zata taba daina yin fim din Hausarba, ta kara da cewa ba ita ya kamata mutane su tambayaba dangane da rashin fitowar tata a finafinaiba.

Masu shirya finafinan da kuma masu bayar da umarni ya kamata mutane su tambaya(domin jin dalilin da yasa basa saka a sabbin finafinai).
Wani yayi kokarin yiwa Maryam gyara inada yace"akwai gyara a maganarki, ki cire kalmar bazab taba daina waba"

Sai Maryam ta mayarmishi da martanin cewa"to bari kaji in gayamaka bazan taba daina yin Hausa fim ba, idan kaga na daina to Mutuwa nayi"

Da alamar cewa wannan tambaya ta yiwa Maryam zafi kuma dama can tana da abin a ranta ta kagara ta amayar dashi.
Sai muce Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment