Sunday, 22 October 2017

Bukola Saraki zai aurawa kirista diyarshi: Hakan ya jawo cece-kuce

Maganar auren diyar shugaban majalisar dattijai Tosin Saraki wadda zata auri wani kirista ta fara jawo cece-kuce, wani me suna Nurudeen Adeyemi ya jawo hankulan mutane akan wannan batu kamar yanda Instablog ya ruwaito, shi wannan Nurudeen yace bai dace ba a addinance da kuma al'adar Arewacin kasarnan ace musulmi ya aurawa diyarshi miji kiristaba.Ya kara da cewa wannan ya nuna cewa Tosin dama tun tuni ba musulma bace watau addinin mahaifiyarta Toyin Saraji take bi kuma be halarta wani malamin addinin muslunci ya daura wannan aureba, amma Nurudeen ya kara da cewa dayake yanzu yawancin malaman 'yan koran siyasa da masu kudine ba mamaki bane idan an daura.

Shidai wannan Aure kamar yanda kafar watsa labarai ta Thisday ta ruwaito za'a daurashine idan Allah ya kaimu ranar ashirin da takwas ga wannan watan da muke ciki a garin Legas, rahotanni sun nuna cewa Baban Amarya Bukola Saraki yaso a kai auren wata kasa inda za'ayi kasaitaccen biki na kece raini amma ita Amaryar tace a Najeriya take so ayi bikin nata.

Nurudeen ya kara da cewa addinin musulunci ya yarda musulmi na miji ya auri kirista mace amma bai yarda mace musulma ta auri kirista na mijiba kuma wannan aure, kamar yanda Nurudeen ya fada zai shafi harkar siyasar Bukola Saraki a Arewacin kasarnan dan za'a rika kallonshi kamar ba daga yankin ya fitoba.

No comments:

Post a Comment