Sunday, 22 October 2017

"Daga yau bazan kara yin wankaba">>inji wata bayan ta hadu da mawaki Tuface

Akwai binda zai saka ka dena wanka? to yau ga wata baiwar Allah ta dau alkawarin cewa ba zata kara yin wankaba a rayuwarta saboda tauraron mawakinnan Tuface Idibia ya rungumeta, ta kara da cewa tabbas duk wanda ya santa yasan cewa tana burin haduwa da fitaccen mawakin, kuma tunda Allah ya hadata dashi to itafa burin rayuwarta ya cika, zata ajiye aikinta ta koma kauyensu da zama.Wannan batu nata ya dauki hankulan mutane sosai musamman a shafukan sada zumunta da muhawara, mutane da dama dai na bayyana soyayyarsu musamman ga fitattun mutane ta hanyoyi daban-daban, misali akwai lokacin da wani masoyin fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ya taba cewa saboda soyayyar da yake mata idan yana da miliyan Dari zai iya bata miliyan casa'in da tara ya rike miliyan daya.

To saidai ita wannan baiwar Allan ko zata iya cika wannan alkawari nata? lura da irin yanda yankinmu na nahiyar Afrika ke da yanayin zafi?


No comments:

Post a Comment