Monday, 9 October 2017

Dan kuka me jawa uwarshi jifa: Yanda wani yaro ya min rugu-rugu da gilashin mota

Dazu da yamma ina cikin gida kawai sai naji kara cus lekowar da zanyi sai naga ashe wani yarone yayi rugu-rugu da gilashin mota na baya dana ajiye a kofar gidan, yaron ya dawo daga makarantane  ya tsaya yana wasa da duste a jikin motar, tsautsai sai zuciya ta rayamai kawai ya buga dutsen a jikin gilashin motar, raina ya baci sosai domin asara bata da dadi, na tausayawa mahaifiyar yaron, wasu yaran iyayensu na barinsu su shagwabe suna abinda sukeso ba'a kwaba musu, haka kuma duk da wasu iyayen basu so amma ya kamata jama'a su rika kwabawa yara idan sukaga suna wani abu daba daidaiba koda kuwa ba 'ya 'yansu bane.


Ta hakane zamu samu al'umma ta gari me tarbiyya domin idan kaki kwabawa dan makwabcinka wai kana tunanin naka shiryayyene tofa zai fito yayi wasa da yawo da wannan wanda kake ganin ba shiryayyeba. Haka kuma idan kaki kwabawa naka saboda soyayya to wataran zai saka kuka.

Allah shi kyauta ya shiryemu baki daya.

No comments:

Post a Comment