Sunday, 29 October 2017

Dan kwallon kafar Ghana Gyan ya zama na farko a nahiyar Afrika da ya bude kamfanin sufurin jirgin sama

Dan kwallon kafar kasar Ghana Asamoah Gyan ya zama dan kwallo na farko a nahiyar afrika daya mallaki kamfanin sufuri na jiragen sama, a ranar Alhamis data gabatane shugaban kasar Ghanar Nana Akufo-Addo yayi jawabi a gurin wani taro inda yace ya samu labari daga majiya me karfi cewa an baiwa dan wasan lasisin bude kamfanin sufurin jirgin sama wanda ya sakawa sunanshi na kiranye watau Baby Jet(BBJ) Airline.Gyan shine dai kyaftin din Ghana kuma ya bugawa kungiyar Sunderland wasa inda daga nan ya koma kasar hadaddiyar daular larabawa da wasa a kungiyar Al-ain, daga nan kuma ya koma buga wasa a kasar China a kungiyar Shangai SIPG, anan ne suka rika biyanshi albashin makudan kudin da sai da ya shiga jerin 'yan kwallon kafa da sukafi amsar albashi me tsoka a Duniya, a wannan shekarar da muke ciki ne Gyan ya koma da buga wasa a kasar Turkiyya.

No comments:

Post a Comment