Sunday, 15 October 2017

Dino Melaye tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin

Sanatan Dino Melaye daya saba yin abubuwan dake daukar hankulan mutane musamman a dandalin sada zumunta da muharawa, ya sake samun wani abin farin ciki daya nunawa Duniya, a wannan hoton Dino Melayenne cikin alamun jin dadi tare da shugaban kasar Rasha, sun dauki hotonne lokacin da 'yan majalisar tarayya sukaje kasar Rashar halartar wani muhimmin taro.Dino Melaye ya saka wannan hoto a dandalinshi na sada zumunta sannan ya rubuta "ina tare da shugaba Putin ya rike min hannu kankam, bashida girman kai".

No comments:

Post a Comment