Sunday, 8 October 2017

"Duk da bani na haifekiba ina miki riko irin na uwa da diyarta">>Hadiza Gabon na murnar zagayowar ranar haihuwar yarinyar da take riko

Wannan itace Maryam, yarinyar da fitacciyar jarumar finafinan Hausa Hadiza Gabon ke rike da ita kamar ita ta haifeta tun bata kai hakaba, Hadizar tayi murnar zagayowar ranar haihuwar Maryam a Yau Lahadi inda tace duk da ba ita ta haifetaba amma ta zama mahaifiyarta kuma tana mata duk wani abu da uwa take yiwa diyarta haka kuma tace ba zata iya misalta irin son da take mataba.Muna taya Maryam murnar zagayowar ranat haihuwarta da fatan Allah ya albarkaci rayuwarta.No comments:

Post a Comment