Sunday, 8 October 2017

"Duk da sanyin da akeyi a Kasar Rasha hakanan zamuje">>Atiku Abubakar ya bada sara ga 'yan Najeriya

Wata magana da tsohon mataimakin shugaban kasa, wazirin Adamawa kuma tsohon dan takarar shugabancin kasarnan Alhaji Atiku Abubakar yayi a dandalinshi  na sada zumunta da muhawara na Twitter ta dauki hankulan mutane sosai ta yanda saida mutane da yawa suka rika kwaikwayarshi, Bayan da Najeriya ta samu zuwa buga wasan kwallon kafa na neman cin kofin Duniya a kasar Rasha sai Atiku ya saka wannan hoton da ake gani a sama ya rubuta cewa "Ance kasar rasha akwai sanyi amma hakanan zamu dunguma muje, ina taya Super Eagles da 'yan Najeriya murna murna.Aikuwa da yin wannan magana tashi sai mutane sukayi ta nuna soyayya anata kwaikwayarshi ta hanyar saka rigar sanyi ana rubuta cewa muma zamuje kasar Rasha kamar Atiku.

No comments:

Post a Comment