Sunday, 8 October 2017

"Duk mijin da zai aureni yasan da cewa zancigaba da fitowa a finafinan Hausa da kuma shiryasu koda bayan nayi Auren>>Maryam Booth


A cigaba da maganarta na cewa bazata daina shirin fim din Hausa ba har sai randa numfashinta ya dauke a Duniya, fitacciyar jarumar finafinan Hausa Maryam Booth ta sake yin karin bayani dangane da hakan yayin da wani ya tambayeta cewa "to tunda kince ba zaki taba daina yin finafinan Hausaba hakan na nufin cewa ba zaki yi Aure ba kenan, ko kuma koda kinyi auren mijinki zai barki kicigaba da sana'arki ta fim?.
Maryam ta mayar mishi da martani inda tace"ni bance bazanyi Aureba, amma koda nayi Aure zan cigaba da fitowa a finafinan Hausa da kuma shiyasu."

No comments:

Post a Comment