Monday, 2 October 2017

Fati Muhammad ta samu karin matsayi a gidauniyar tallafawa marasa galihu ta Atiku Abubakar

Tsohuwar fitacciyar jarumar finafinan Hausa Fati Muhammad ta samu karin matsayi a gidauniyar tallafawa masu karamin karfi da marasa galihu ta tsohon mataimakin shugaban kasa, Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, a da dai Fatin itace shugabar kula da harkokin mata ta gidauniyar a jihar Kaduna yanzu kuma saboda jajircewa da nuna kwazo da ta nuna a aikin nata an kara mata matsayi zuwa shugabar harkokin mata me kula da yankin Arewa maso yamma.Muna tayata murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment