Friday, 13 October 2017

Fim din da Rahama Sadau ta shirya na Rariyane ya lashe kyautar fim da yafii yin fice a shekarar 2017.

Lallai idan Allah ya riga ya amsawa mutum to babu wani abinda zai hana mutum kaiwa ga inda Allah ya kaddaramishi zuwa na cigaba a Rayuwa, wani abin farin ciki ya sake samun fitacciyar korarriyar jarumar finafinan Hausa wadda yanzu take taka rawar gani a finafinan kudu watau Rahama Sadau, bayan da aka koreta daga masana'antar Finafinan Hausa na Kannywood Rahama sai ta koma gefe ta daddage ta shirya wani sabon fim da kanta wanda ta sakawa suna Rariya, tun kamin fitowar fim din wakar cikin fim din wadda Umar M Sharif ya rera ta sayar da fim din kuma haka Rahama ta saka kwazo wajan ganin ta tallata fim din zuwa manyan jihohin kasarnan to a yanzu dai wannan fim na Rariya ya samu kyautar fim da yafi yin fice a shekarar 2017 daga masu bayar da kyaytuka na City People Awarda.
Wannan kyauta da fim din Rariya ya lashe batazo da mamakiba ganin irin kokarin da Rahama tayi na tallatashi a idon Duniya, Rahama tayi ta bin gidajen silma-silma na manyan jihohin Arewa wajan ganin ta tallata wannan fim nata kuma koda mutum bai kallaba yaji wakar fim din Rariya. Muna tayata murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment