Sunday, 29 October 2017

Garin dake ake neman mutane su zauna a ciki: za'a biyaka kudi naira dubu dari takwas idan ka yarda ka koma da zama garin: Shekaru Ashirin kenan ba'a taba kama koda mutum daya da laifi ba a garin

Garin Candela dake kasar Italiya ya kusa zama kufai domin kuwa babu mutane sosai a garin sai tarin gidaje da tsuntsaye da kwarika keta shawagi a ciki, matasan garin duk kusan sun tsere sai tsofaffine ke zaune a garin, a shekarun 1990 akwai mutane fiye da dubu takwas a wannan gari amma yanzu duka-duka wadanda ke zaune a garin basu wuce mutum dubu biyu da dari bakwai ba kuma duk tsofaffi.

Domin farfado da wannan gari, magajin garin, Nicola Gatta ya saka kudi da suka kai dalar Amurka dubu biyu da dari uku da hamsin kwatan-kwacin sama da naira dubu dari takwas kenan a Nairar Najeriya ga duk wanda ya yarda ya koma garin da zama.

Wani na hannun damar magajin garin Candela yace yanda aka tsara abin shine idan mutum yazo be da mata ko abokiyar zama to za'a bashi kudi Yuro dari takwas, kwatan-kwacin sama da naira dubu dari uku kenan, idan kuma kazo da mata ko abokiyar zama za'a biyaka Yuro dubu daya da dari biyu kusan Naira dubu dari biyar kenan, idan kuma iyali suka zo da mutane uku to za'a basu Yuro dubu daya da dari biyar zuwa Yuro dubu daya da dari takwas, kwatan-kwacin Naira dubu dari shida zuwa dubu dari bakwai kenan, idan kuma iyali suka zo da mutane hudu to shine za'a basu Yuro dubu biyu ko kuma sama da haka, kwatan-kwacin Naira dubu dari takwas kenan.

Sharuddan bayar da wannan kudi guda uku ne:

Na daya shine dole mutum ya koma da zama garin Candela.

Na biyu kuma shine ya kama gidan haya inda zai zauna a cikin garin.

Na uku shine dole sai mutum yana da aikin yi da ake biyanshi akalla Yuro dubu bakwai da dari biyar a shekara, kwatan-kwacin sama da Naira miliyan uku kenan ko kuma muce dubu dari biyu da hamshin da takwas duk wata.


Na hannun damar magajin garin ya kara da cewa basa son mutanen da zasu so su zamar musu nauyi ko kuma mutum yayi tunanin su zasu rika bashi kudin kashewa, duk wanda zai zo dolene ya zamana yana da aikin yi, yana samun kudin shiga.
Haka kuma ya kara da cewa suna da zaman lafiya sosai domin shekaru ashirin da suka gabata ba'a taba samun wani da laifin karya doka ba koda sau daya, kuma akwai abubuwan birgewa, babu hayaniya akwai guraren sayar da abinci kala-kala da kuma bukuwa da ake shiryawa a garin dan debewa mutane kewa.
Yanzu haka dai ance iyalai shidahar sun koma garin da zama, kuma wasu guda biyar sun nemu a basu damar zama a garin.
CNN

No comments:

Post a Comment