Friday, 13 October 2017

Gidan talabijin na Arewa24 yaji dadin yanda hirar da Momo yayi da Umma shehu ta watsu

Gidan talabijin na Arewa24 wanda a cikinshine Aminu Sharif Momo yayi hira da Jaruma Umma Shehu wanda a cikin hirar ya tambayeta matar data shayar da Annabi amma bata bayar da amsaba dalilin haka wanna hira ta karade shafukan sada zumunta da Muhawara akayita tattaunawa me zafi akai, to yanzu dai Momo ya fito ya bayyanawa Duniya cewa babu inda ita Umma Shehun ta bayyana cewa batasan amsar wanna tambayar da yayimataba, yace kawai aikin wasu makiyan masana'antar finafinan Hausa ta Kannywoodne suka yanke inda sukeso suka watsawa Duniya domin tozartawa.


Haka shi kanshi Gidan talabijindin ya fito ya nuna jin dadinshi akan irin yanda hirarta watsu domin kamar yanda bidiyonnan nakasa yake nunawa gidan talabijindin ya kara samun mabiya a shafukan sada zumunta da muhawara sannan kuma an samu karin wadanda suka kalli wannan hoton hirar da yawa sannan kuma ita kanta Umma shehun ta samu karin mabiya a dandalinta na sada zumunta kamar dai yanda gidan talabijindin ya bayyana.

Wannan yana nuna cewa gidan talabijindin ya samu karuwa ta hanyar watsuwar wannan hira.

Domin ji da fahimtar cikakken wannan labari sai a kalli hotunan bidiyonnan guda uku. 

To saidai ga dukkan alamu a gurin ita jaruma Umama Shehu zancen ba haka yakeba, Domin akwai almun damuwa tattare da ita, bataji dadin watsuwar wannan hirarba da kuma irin yanda mutane suka mata fassaraba, domin kuwa ta saka wani hoto a dandalinta na sada zumunta bayan faruwar wannan lamarin tana fadin cewa "wani hanin ga Allah baiwane" kuma a duk lokacin data saka wani sha'ani nata a dandalinta na sada zumunta sai an samu wasu suna kiranta da Jahila.


No comments:

Post a Comment