Monday, 9 October 2017

Gwamna Aminu Tambuwal ya karrama hazikin soja Ahmad Buhari Bature


Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya karrama sojannan wanda yayi zarra a cikin sojojin da suka kammala makarantar horar da sojoji dake Kaduna da ake kira da NDA a takaice me suna Ahmad Buhari Bature. Gwamnan yayi kira ga mutane dasu rika baiwa sojoji hadin kai a ayyukan da sukeyi na tsaron kasa kuma ya bayyanasu a matsayin daya daga cikin jami'an dake taimakawa wajen kara kawo hadin da dunkulewar Najeriya a matsayin kasa daya.Gwamna Tambuwal yayi kira ga Ahmad daya lura daga inda ya fito gurine da aka sanshi da kamala da kima saboda haka yayi kokari dan ganin shima duk inda ya samu kanshi ya kare martabar kanshi ta gidansu da kuma al'ummar daya fito daga ciki.

No comments:

Post a Comment