Saturday, 14 October 2017

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya halarci sallar Juma'a

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya halarci sallar Juma'a  jiya Juma'a a masallacin garin Ekitin, hakan yana daya daga cikin shirye-shiryen shagulgulan bikin murnar cikar kwamnan shekaru uku akan kujerar Gwamna, mutane da yawa sunyi mamakin ganinshi a masallacin kasancewarshi kirista amma wannan ba shine karo na farkoba da gwamnan yake halartar sallahba.Koda ranar babbar sallah data gabata gwamnan ya halarci sallar idi sanye da rawani saikace wani shehin malami.
No comments:

Post a Comment