Thursday, 26 October 2017

"Har yanzu motocina na kashin kaina nike hawa">>Matar Shugaban kasa A'isha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta karyata ikirarin sanata Misau na cewa da yayi wai Shugaban 'yan sanda Ibrahim Idris ya siya mata sabbin motocin alfarma guda biyu ba bisa ka'idaba, A'isha ta bayyana a dandalinta na sada zumunta da muhawara na shafin twitter cewa ita fa har yanzu da motocinta na kashin kanta take zirga-zirga.


Ga dukkan alamu akwai wata jikakkiya tsakanin shugaban 'yan sanda Ibrahim Idris da Sanata Misau wanda ada can baya shima dan sandanne kamin ya shiga siyasa domin sai jifan juna suke da zarge-zarge.

Domin kuwa Misau ya kara wani zargin akan wannan inda yace Idris din ya canja shekarun da ya kamata ya ajiye aiki kuma ya ta ba yiwa wata 'yar sanda ciki amma ya lullube abin, da ga baya ma har ya aureta.

Allah shi kyauta

No comments:

Post a Comment