Monday, 30 October 2017

Hoton barkwanci akan batun MainaBatun yaki da cin hanci da rashawa karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ya sake daukar sabon salo ganin yadda jama’a da dama ke baiyana takaici kan ikirarin gwamnati na yaki da munmunar akidar cin hanci amman kuma lamarin ba haka yake ba a zahiri,  sabuwar badakalar da ta kunno kai da ta haifar da cece-kuce a kasar shi ne matakin shugaba Buhari na mayar da AbdulRasheed Maina kan mukamin darekta a ma’aikatar cikin gida duk kuwa da tarin zarge-zarge da ake yi wa Maina na yin almundahana da kudaden gwamnati a yayin da yake rike da mukamin shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasa.


Kafar watsa labarai ta DWhausa tayi wannan zane na barkwanci akan bataun.

No comments:

Post a Comment