Thursday, 19 October 2017

Hoton barkwanci akan kudun tallafin da gwamnatin tarayya take baiwa jihohin kasarnan


A ‘yan kwanakin nan ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya bayyana mamakin yadda wasu ma’aikatan gwamnati a jihohin kasar ke rayuwa sakamakon rashin biyansu albashi da ake yi.Wannan matsalar ta rashin biyan albashin dai na janyo matsaloli masu yawa a jihohin da abin ya shafa, duk da cewar gwamnatin tarayya ta ce ta samar da kudaden da gwamnatocin jihohin za su iya warware matsalar.

Haka kuma yanzu maganar da ake gwamnonin sun sake lallabowa gurin shugaba Buhari akan ya kara musu wasu kudin, wannan wani hoton barkwancine da kafar watsa labarai ta DW Hausa tayi akan wannan batu.

No comments:

Post a Comment