Monday, 23 October 2017

Hoton ma'aurata suna shakatawa a gabar teku ya dauki hankula saboda irin kayan da matar ta saka

Allah sarki a lokacin da wasu mata ke saka kaya masu matse jiki da nuna surar jikkunansu  musamman idan akace za'ayi fitar yamma ko zuwa wani gurin shakatawa, wannan bawan Allahn da rahotanni suka nuna cewa matarshice sunje shakatawa bakin ruwa kamar yanda masoya keyi a inda ake da irin wannan gabar ruwan, abinda ya dauki hankulan mutane shine irin kayan da matar tashi ta saka.An saba ganin mata tsirara-tsirara a gabar ruwa irin wannan to amma abin alfahari ga wannan iyali da kuma dukkan musulmin Duniya sai gata cikin kaya masu suturta jiki kuma hakan bai hanasu yin annashuwa ita da mijin nataba.

Wasu sun rika yin maganganun batanci na cewa wai 'yan kauyene ma'auratan amma mu munsan wannan ba kauyanci bane, muna musu fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment