Wednesday, 11 October 2017

Hoton yaro yana rubuta jarabawa ya daukin hankali

Wannan hoton na wani yaro zufa nata ketomai yana rubuta jarabawa ya karade shafukan sada zumunta da muhawara, da yawa na tambayar wai wace irin jarabawace yake rubutawa da tayi zafi haka? Toh jama'a Duniyafa kenan mutum dan uwanka ya maka tambaya ka shiga cikin irin wannan hali inaga ace mala'iku ko kuma mahaliicinkane yake maka tambaya?


Wannan yasa na tuno da wani labari makamancin wannan da ya taba faruwa dani, akwai wani bawan Allah shugaban wata sananniyar kungiya da mutane da yawa suke karkashinta to akwai 'yar uwata wadda itace shugaban bangaren mata na wannan kungiya, sai suka samu rashin fahimta da shugaban nasu, da yawa daga cikin wadanda suke karkashinshi suka bijiremai, a kokarinshi na hada kansu sai ya kirani yake gayamin yanda abubuwan suka faru, maganarshi da tafi daukar hankalina itace inda yake cemin "malam mutanennan tambayoyi dari suka shiryamin wai in basu amsa, in ba so suke zuciyata ta buga in mutuba, wane irin tashin hankaline wannan?" to mutum dan uwanka fa kenan ya maka tambaya duk karude inaga mahaliccinka wanda yace maka duk wani abu dakayi na alheri ko na sharri daidai da kwayar zarra sai ka ganshi?

Tabbas tambayoyin kabari dana ranar kiyama wallahi taimakon Allahne kawai da rahamarshi da jinkanshi zai bamu ikon amsasu mu samu rabauta, ya Allah ka rufa mana siri Duniya da lahira.

No comments:

Post a Comment