Monday, 30 October 2017

"Idan shugaba Buhari ya tsaya takara a 2019, to tabbas shine lashe zaben">>Bashir Ahmad

An samu wani bawan Allah dake sukar gwamnatin shugaba Buhari a dandalin sada zumunta da muhawara na shafin Twitter inda mutumin yayi ikirarin cewa a shekarar 2019 idan Allah ya kaimu irin tallar da irinshi-irinshi zasu yi dan ganin sun bata shugaba Buhari, sai ya kwammace dama bai zama shugaban kasa ba.

Mutumin ya kara da cewa dokar hana yiwa wani batanci/kalaman kiyayya da aka saka cikin doka ba za ta hanasu yin wannan tallarba.

To saidai me baiwa shugaban Buharin shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya yiwa wannan mutumin martani inda ya gaya mishi cewa....ka rubuta ka ajiye, idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar tsayawa takara a shekarar 2019, to tabbas shine zai lashe zaben.

Wannan batu ya dauki hankalin mutane.


No comments:

Post a Comment