Sunday, 15 October 2017

Ikon Allah:Kalli yanda wuta keci a cikin wata bishiya/Itaciya amma bata fadiba

Allah sarkin sarauta meyin yanda yaso, a satin daya gabatane aka samu wata mummunar wutar daji a Jihar California ta kasar Amurka wadda akayi kiyasin cewa ta kashe mutane goma sha bakwai kuma ta kone gidaje dubu biyu,  bayan wannan wutar daji ta lafa sai wani mutum ya fito daga inda yake boye yana neman hanyar da zata fitar dashi daga yankin da wutar dajin ta auku, aikuwa yana cikin tafiya sai yaga wani abin al'ajabi wanda yace tunda yake bai taba ganin abinda ya bashi mamakiba irinshi, bishiya/itaciyace gata a tsaye amma wuta naci a cikinta, watau cikin bishiyar/itaciya yanata ci da wuta amma bata fadiba, kamar yanda ake iya gani a wannan hoton.Hakan ya sashi ya tsaya ya dauki gajeren hoton bidiyon yanda bishiyar/itaciyar ke cin wuta dan ya nunawa Duniya irin abin mamakin daya gani.

Kafar watsa labarai ta CNN ta samu wannan bidiyo.

No comments:

Post a Comment