Sunday, 8 October 2017

JAN HANKALI: Rayuwar Duniya Abar Tsoro Ce


Komai yawan dukiyar ka, komai yawan dangin ka, ba su isa su saya maka gida a Aljanna ba (Su ma ta kansu suke yi).

- Rowa bata hana arzikinka karewa.. Cuta da ha'inci da zalunci ba su sanya dukiyar ka ta karu. Sai dai su kara maka nauyin hisabi..

- Rayuwar duniya mafarki ce amma lahira ita ce tabbas. Mai hankali shi ke rabuwa da duniya tun kafin ta bar shi.
- Dan Adam ba komi bane face turbaya, ka gama kwambonka cikin kasa zaka koma.

- Duk daren dadewa mutuwa sai ta riske ka, dukiya, jin dadi, tsanani, kunci ko wadata ba za su sanya makusanta zama da gawarka ba. (Makabarta za su kai ka)

Allah kasa muyi kyakkyawar karshe.
rariya.

1 comment:

  1. Wanann haqiqanin gaskiya ce ! Allah dai ya sa mu gane mu kuma canza tun kafin lokacin nadama ba ta amfani

    ReplyDelete