Wednesday, 25 October 2017

"Ka koyawa Rahama Sadau tarbiyya maimakon dawo da ita harkar fim">>Musbahu ya gayawa Ali Nuhu


Fitaccen mawakin Hausa Misbahu Ahmad yayi kira ga Ali Nuhu dacewa maimakon yayi kokarin dawo da Rahama Sadau harkar fina-finan Hausa kamata yayi ya koyamata tarbiyya da sanin darajar kanta a matsayinta na mace da kuma sanin datajar mutane.Gadai abinda Misbahu ya rubuta a dandalinshi na sada zumunta na Faceboom.

"Hmmmm! Ali Nuhu ni shawarar da zan baka, da ka tsaya kana kokarin sai ka dawo da Rahma Sadau, me zai hana ka yi kokarin ganin ka ba ta tarbiya ta wajan sanin darajar kanta na 'ya mace kuma musulma, da kuma sanin darajar mutane, ka koya mata iya magana. Ka sani fa cewa ita mace ce uwar al'umma ce wataran, kar ka manta gidan aure za ta je, za ta zama uwar wasu ita ma!!!"

No comments:

Post a Comment