Tuesday, 10 October 2017

Kalli sabon saurayin Maryam Booth


Idan masu bibiyar shafin hutudole.com basu mantaba .a watanni kusan shida da suka gabata mun kawo muku labarin yanda saurayin fitacciyar jarumar finafinan Hausa Maryam Booth ya yaudareta har ta kasa daurewa ta fito dandalinta na sada zumunta ta bayyana irin yanda takeji(idan baka karanta labarinba danna nan), haka kuma watanni biyu da suka gabata mun kawo muku labarin yanda Maryam ta fadi cewar bata da saurayi kuma tana cikin farin ciki (idan baka karanta labarinba danna nan)to yanzu Allah ya tarfawa garinta nono domin kuwa da alama ta samu wani sabon zankadeden saurayin ya fito yace yana sonta kuma suna buga soyayya ta jin dadi. Maryam kenan da sabon saurayinta a wannan hoton na sama.


Maryam ta saka hotunanta tare da wannan saurayi a dandalinta na sada zumunta da muhawara tayi rubutu kamar haka:

"Ka shigo cikin rayuwata ka gayaramin ballallar zuciyata(watau ya dawo mata da ruhin soyayya cikin zuciyarta wanda tayi rashinshi a baya) ka gyara dukkan wani rauni da yake tare dani kuma ka fahimtar dani yin soyayya ta gaskiya ba tare da tsoroba, domin zagayowar ranar haihuwarka ina mika godiyata gareka akan abubuwan dakamin, ina tayaka murnar zagayowar tanar haihuwarka. Nawa......"
Wadannan hotuna nasu tare da kuma maganganun da Maryam ta rubuta alamomine masu karfi dake nuna cewa ita da wannan saurayin suna soyayya. Muna musu fatan alheri da kuma Allah yasa suci ribar soyayyar.
No comments:

Post a Comment