Friday, 27 October 2017

Kallon da Abba Kyari kewa Bukola Saraki a wannan hoton ya dauki hankulan mutane

Mutane sun rika tabayar me ke faruwane tsakanin shugaban ma'aikata na shugaba Buhari watau Abba kyari da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki?, wannan tambayar ta tasone dalilin wannan hoton na sama da ya watsu, inda Abba Kyarin yake wa Bukola Saraki wani irin kallo me cike da alamomin tambaya.


Mutane sunyi sharhi daban-daban akan wannan hoto inda wasu suka bayyana cew irin wannan rashin jituwa tsakanin manyan jami'an gwamnati da kuma burin wasu na kusa da Buharin na ganin sun saka son ra'ayinsu a harkar gwamnati yake kawo wa Shugaba Buharin cikasa a wasu al'amura.


No comments:

Post a Comment